5 Afirilu 2020 - 07:25
Fiye Da Iraniyawa Miliyan 69 Ne Aka Yi Wa Gwajin Gano Cutar “Corona”

Mataimakin ministan lafiya na Iran Ali Reza Ra’isy ne ya bayyana cewa; fiye da mutane miliyan 69 da dubu dari biyu aka yi wa gwajin gano cutar ta “Corona’ a karkashin bincike na gama-gari da ake yi.

(ABNA24.com) Mataimakin ministan lafiya na Iran Ali Reza Ra’isy ne ya bayyana cewa; fiye da mutane miliyan 69 da dubu dari biyu aka yi wa gwajin gano cutar ta “Corona’ a karkashin bincike na gama-gari da ake yi.

Jami’in na ma’aikatar kiwon lafiyar ya kara da cewa; A tsakanin wannan adadin na mutane, an yi wa mutane miliyan 57 binciken na kai tsaye, yayin da sauran miliyan 12 su ka yi wa kansu gwaji ta hanyar shafin internet na musamman da ake da shi.

Har ila yau Ali Riza ya yabawa yadda al’ummar Iran din su ke bayar da hadin kai wajen killace kawuka da takaita kai komo, musamman a cikin makon da ya shude,tare da yin kira da su ci gaba da bayar da wannan hadin kan.

Ya zuwa jiya Juma’a an tabbatar da cewa adadin wadanda su ka kamu da cutar ta Corona a Iran sun kai dubu 53 da 183, sai kuma dubu 17 da 935 da su ka warke, yayin da wasu dubu 3 da 294 su ka mutu.


/129